Manufar Sirri na Premise

Aiki daga:  April 1, 2024

Mu a Premise Data Corporation (“Premise”) muna damuwa da yadda ake amfani da watsa bayanan ku, kuma mun dauki sirrin ku da muhimmanci. Ku karanta wannan domin sanin yadda muke karba, amfani da watsa bayanai. Duk wata kalma mai manyan harufa da mukayi amfani dashi a wannan Manufan Sirri batare da ayyanawa ba suna da bayanin su acikin Ka’idojin Amfani:https://tos.premise.com/terms-of-use/.

Idan kuka shiga ko kuma amfani da Aikin, hade da amfani da shafin, dandali ta ko wanne hali ko sauke manhajojin wayar mu, dubawa da kamala Aiyuka (kamar yadda aka kwatanta a Ka’idojin Amfani) da kuma yin rajistar Asusun Premise, kun amince da aiki da ka’idojin wannan Manufar Sirri, kuma kun yarda da karba, amfani da yada bayanan ku harda hotuna, bidiyo, rikodin, hoto tare da hoton allon waya, a hanyoyin da aka jera a kasa.

Ka Fahimci Aikin Ka Awajen Mu kumar haka

Premise yana amfani da kalmomin “Customer”, “Contributor”, da “Visitor” a wannan manufa domin kwatancen ayyukan da suka danganci Premise da ayyukan sa da muhalli. An ayyana wadannan ayyukan kamar haka:

    • Customer: Idan kai wanda yake aiwatar da Yarjejeniyar Manyan Ayyuka ko wani yarjejeniyar abokin ciniki tare da mu (“Yarjejeniyar Abokin Ciniki”) ( ko ma’aikaci/mai bada shawara na kamfani da ya aiwatar da irin wannan Yarjejeniyar Abokin Ciniki tare da mu ko kuma kana amfani da ayyukan mu a matsayin ma’aikaci/mai bada shawara), ko wanda Premise ya ba izinin shiga cikin daya daga cikin dandalin abokin ciniki na yanar gizo, an ayyana ka a wannan Manufar Sirri a matsayin Customer.
    • Contributor: Idan kun dauko manhajojin mu, ana ayyana ku a wannan Manufar Sirri a matsayin contributor.
    • Visitor: Sauran mutane kuma an ayyana su a matsayin Visitor.

Kalmomi a Kashi na I na wannan Manufar Sirri yana magana akan Abokan Ciniki, Masu Bada Gudunmawa da Baki. Kalmomin Kashi na II na magana akan Customer. Kalmomin Kashi na III yana magana idan kai Contributor ne. Kalmomin Kashi na IV yana magana akan Masu Bada Gudunmawa da Baki wadanda suke zaune a Jahar California kuma, ko wasu jahohin da suke bada irin wannan damar

 

KASHI NA I – KALMOMI DA YAKE MAGANA AKAN KOWA
Abokan Ciniki, Masu Bada Gudunmawa Da kuma Baki


Wannan Manufar Sirri yana aiki a manhajojin Premise, shafukan yanar gizo, dandali, ka ayyuka da kayayyakin da suke cikin manhajoji, shafukan yanar gizo da sauran dandalin yanar gizo. Premise yana karbar bayanai game da ku lokacin da kuka dauko manhajar mu na waya da kuma wasu huldodi da sadarwa da kukeyi da mu ta yanar gizo (harda shafi, dandali da dandamali) ko bahaka ba. Ku tuna cewa amfani da kukeyi da Ayyukan a ko yaushe yana tare da Ka’idojin Amfani, wanda ya hada da wannan Manufar Sirri. Premise ne ke da alhakin gudanar da Aikin, kuma wannan Manufar Sirri yana aiki akan bayanai da Premise ya karba da amfani dasu.

Za mu iya tura bayanan da muka ayyana acikin wannan Manufar Sirri zuwa, da sarrafawa da ajiyewa, a Kasar Amurka, wanda zai iya kasancewa babu karfin kariyar bayanai kamar kasar da kuke. A inda aka samu hakan, zamu dauki matakai da suka dace domin ba bayanan ku kariya bisa wannan Manufar Sirri da dokokin da suka dace.

Muna kokari a koda yaushe wajen inganta Ayyuka. Za mu iya canja wannan Manufar Sirri lokaci-lokaci. Za mu sanar da ku canje-canjen ta hanyar tura muku sakonni ta sakon cikin manhaja, saka sako akan dandalin sada zumuntar mu, saka sabon Manufar Sirrin a shafin yanar gizon mu, dandamali, dandalin yanar gizo da/ko wasu hanyoyin. Ku lura cewa idan kun fita daga tsarin samun sakonnin sanarwa ta imel daga wajen mu (ko baku bamu adireshin imel dinku ba), wadannan sanarwar dokar duk da haka yana cikin amfani da Aikin, kuma har yau hakkin ku ne karantawa da fahimtar su. Idan kunyi amfani da Aikin bayan saka canje-canjen Manufar Sirrin, hakan yana nufin kun amince da duka canje-canjen. Amfani da bayanan da muka karba ya danganci Manufar Sirri da yake aiki a lokacin da aka karbi bayanan

IYAKA DA INDA YAKE AIKI

Wannan Manufar Sirri yana aiki akan mutane da suke shiga ko amfani da duk wani Ayyuka a ko ina a fadin duniya.

A sanin mu bama nema ko karbar bayani daga wani wanda yake kasa da shekaru 18, ko dokar shekaru mafi karanci a inda mutum yake zaune ko yake lokacin da yake amfani da Ayyukan, ko da kuwa yayi kadan (gabaki daya, “Shekaru Mafi Karanci”). Ku lura kada kuyi kokarin yin amfani da Aiki ko tura wasu bayanai game da kan ku zuwa wajen mu idan shekarun ku basu kai Mafi Karanci ba, kuma kada ku tura duk wani bayanai akan wani wanda shekarun sa bai kai Mafi Karanci ba ko kasa da shekara 13, wanda yafi kasa. Idan muka gano cewa mun karbi bayanan wani wanda bai kai shekaru Mafi Karanci ba ko shekara 13, wanda yafi kasa, za muyi gaggawar goge bayanan da sauri. Idan kunyi imanin cewa wani wanda yake da shekaru kasa da Mafi Karanci ya bamu bayanan kan sa, ko idan an bamu bayanai game da wani wanda yake kasan shekaru Mafi Karanci na 13, wanda yafi kasa, ku tuntube mu a [email protected]

KARBA DA KUMA AMFANI DA BAYANAI

Bayanai Da Muke Karba Ta Hanyar Amfani Da Kukeyi Da Aiki

Muna karbar bayanai akan yadda kuke mu’amala da Aikin, zabubbukan da kuka bayyana, da saitukan da kuka zaba. A wani lokacin, munayin hakan ne ta amfani da kaskon cookies, pixel tags, da fasahohi masu kama da haka da suke kirkira da rike manuni na musamman. Ta hanyar cookies da muke sakawa a manhajar yanar gizo ko na’urar ku, muna iya karbar bayanai akan abubuwan da kukayi a yanar gizon bayan kun fita daga Aikin. Wannan bayanin yana bamu damar inganta Aikin da saita yanayin yanar gizo, da kuma yadda aka kwatanta a wannan Manufar Sirri.

Kuma muna karbar bayanai da kuka bamu kai tsaye, tare da bayanai da kuka bayar ta amfani da asusun wasu na waje.

Manhajar shiga yanar gizon ku zai iya baku zabin “Do Not Track”, wanda yake baku damar yin nuni ga masu sarrafa shafukan yanar gizo da manhajojin yanar gizo da ayyuka (harda halayen ayyukan talla) da baku son irin wadannan su dinga bin diddigin ayyukan da kukeyi akan yanar gizo na lokaci da kuma sauran shafukan. Wannan Aikin baya aiki da siffar “Do Not Track” na manhajar yanar gizo a wannan lokacin, hakan yana nufin muna karbar bayanan ayyukan da kukeyi akan yanar gizo a duka lokacin da kuke amfani dashi da lokacin da kuka bar Aikin. Idan kukayi amfani da Aikin, kun amince da wannan karbar bayanan.

Google, Bing, da tallece-tallecen shafukan zumunta, da wasu masu dillanci irin wadannan da Premise ke aiki dasu, zasu iya karba ko amsar bayanai masu nuni da ayyukan da kukeyi akan yanar gizo na wani lokaci ko akan wasu shafukan daga Aikin da wasu manhajoji, da yin amfani da wannan bayanan domin bayar da magwajin ayyuka da tallece-tallece. Idan kukayi amfani da Aikin, kun yarda da karba da amfani da bayanan domin daidaita talla. Zaku iya fita daga tsarin Google Analytics ta amfani da wannan https://tools.google.com/dlpage/gaoptout/.

Muna amfani da analytics domin taimakawa wajen sarrafa yadda masu amfanin mu zasuyi amfani da Aiki. Google Analytics yana amfani da kaskon cookies domin karbar bayanai irin kamar sau nawa mai amfani yake shiga Aikin, wasu shafuka yake zuwa, da wasu shafuka yayi amfani dasu kafin zuwa Aikin. Zamu iya amfani da bayanan da muka samu daga Google Analytics domin inganta Aikin ko mu tura muku sakonnin talle game da Aikin mu. Google Analytics yana karbar adireshin IP da aka baku a kwanan watan da kuka ziyarci Aiki, amma ba sunan ko wani bayanan kan ku ba. Ba ma hada bayanan da aka samo ta amfani da Google Analytics da duk wani bayanan da yake bayyana ku. Koda yake Google Analytics yana dasa kaskon Cookie domin gano ku a matsayin mai amfani na daban a lokaci na gaba idan kun ziyarci Aikin. Babu wanda zai iya amfani da wannan Cookie sai Google. Iyawar Google na amfani da watsa bayanai da Google Analytics ya karba game da ziyarar Aikin an dakatar dashi ga Ka’idojin Amfani da Manufar Sirri na Google. Zaku iya samun karin bayani game da Google Analytics a http://www.google.com/policies/privacy/partners/.

 

A inda ake bukatar mu nemi yardar ku domin yin amfani da kaskon cookies marasa-muhimmanci a karkashin dokoki, zamu nemi wannan yardar ta wajen lura da kaskon cookies namu.

Karin Bayani

Kuyi kokari ku duba sashoshin da ke kasa a wannan Manufar Sirri da ya dangance ku domin bayyanarwa game da karin bayanan da muke karba

RIKE BAYANAI

Zamu ajiye bayanan ku ne kadai na tsawon kammala bukatun da yasa muka karba, harda dalilan gamsarwar dokoki, tsari, haraji, lissafin kudi ko bukatun rahoto. Zamu iya rike bayanan ku na tsawon lokaci idan aka samu korafi ko idan mukayi imanin akwai wani kara tsakanin dangartakan mu da ku. Domin kayyade lokacin da yafi dacewa na rike bayanan ku, muna la’akari da yawa, yanayi da muhimmancin bayanan naku, samun hatsarin cutarwa daga amfani babu izini ko bayyana bayanan naku. Dalilan da yasa muke sarrafa bayanan naku da kuma ko zamu cimma wadannan dalilan ta wasu hanyoyi, da kuma hade da dokoki, tsari, haraji, lissafin kudi ko wasu bukatu.

KARIYAR BAYANAI A TURAI

Wannan sashe yana aiki akan karbowa, karba ko sauran sarrafawa ko a madadin mu wajen karbar bayanan ku da European Economic Area (“EEA”) da/ko United Kingdom (“UK”).

Za muyi kokarin sarrafa bayanan ku bisa tanadin dokoki sirri, harda batare da iyaka ba, inda ya kamata, General Data Protection Regulation (Regulation (EU) 2016/679) (“EU GDPR”), EU GDPR sabida sashe ne na dokokin kasashen Ingila da Wales, Scotland da Northern Ireland a cikin sashen dokar European Union Withdrawal Act 2018 (“UK GDPR”), the UK Data Protection Act 2018, da Sirrin  Electronic Communications (EC Directive) Regulations 2003 (the “European Data Privacy Laws”).

Ga cikakken bayani akan bayanan ku da muke sarrafawa, damar da muke dasu bisa doka na sarrafawa da yadda muke yada bayanan ku a kasan nan 

A karkashin Dokokin Bayanai na Turai, kai, a matsayin ka na mai bayanin, kuna da wadannan daman:

    • Neman shiga ganin bayanan ka.
    • Neman gyaran bayanan ku da muke dashi.
    • Neman a goge bayanan ka.
    • Kin yarda da sarrafa bayanan ka.
    • Neman dakatarwa wajen sarrafa bayanan ka.
    • Neman canjin wuri ga bayanan ka gare ka ko a waje.
    • Janye izini a ko wanne lokaci inda muke bukatar izini wajen saffara bayanan ka

Domin samun duka wadannan damar, ku tuntube mu ta bayanan mu da muka bayar a kasa. Za muyi kokarin amsa muku acikin wata daya bayan samun rokon, saidai idan rokon yana da wahala, shine zai iya daukar lokacin ma tsawo. Kuma zamu iya neman karin bayani na musamman daga gare ku domin tabbatar da ku da damar ku na samun bayanai (ko samun wani damar). Ku sani cewa akwai abubuwa da ake iya kara da cirewa daga wadannan dokokin, wadanda za muyi amfani dasu bisa Dokokin Bayanai Na Turai suka bayar. Musamman, idan kun bayar da aminci da kuma janyewa, zamu iya sarrafa bayanin a wajen da doka ta bamu damar yin hakan.

Zamu iya fitar da bayanan mutum da muka sarrafa acikin EEA ko UK zuwa wajen EEA ko UK, harda kasar Amurka. Bayanan ka kadai za’a fitar a wajen EEA ko UK, inda ya dace, bisa Dokokin Sirri na Turai, wanda zai iya hadawa da karin wasu dokokin ko matakai da aka dauka ko yadda a ofishin Kwamishinan Bayanai na kasar UK ko Tarayyar Turai ko wasu hukumar EEA.

TUNTUBE MU

Idan kuna da wasu tambayoyi game da wannan Manufar Sirri, ku tuntube mu ta [email protected] ko yi mana wasika zuwa Premise Data Corporation, Inc., Attn: Legal, 405 W 13th street, 3rd floor, New York, NY 10014, United States of America ko adireshin wakilan kare bayanan mu da muka saka a kasa.

Mun nada wadannan wakilan kare bayanai a kasar UK da kuma EEA wadanda, harda wasu dawainiya, zasu iya karbar sako daga gare ku a madadin mu ko hukumar da tadace:

    1. United Kingdom:
      Adam Brogden [email protected]
      Tel +44 1772 217800
      1st Floor Front Suite
      27-29 North Street, Brighton
      England
      BN1 1EB
    1. European Economic Area:
      Adam Brogden [email protected]
      Tel +35315549700
      INSTANT EU GDPR REPRESENTATIVE LTD
      Office 2,
      12A Lower Main Street, Lucan Co. Dublin
      K78 X5P8
      Ireland

Idan kuna ganin cewa bamu iya magance tambaya ko damuwar ku ba ko kuma kunaso yin haka, kuna da damar yin korafi a karkashin Dokokin Sirrin Bayani na Turai tare da hukumar kariyar bayanai EEA ko UK, a inda ya dace. Ya danganki kasar UK, zaku iya tuntubar Ofishin Kwamishinan Bayanai na UK www.ico.org.uk.

KASHI NA II – KARIN KA’IDOJI DOMIN ABOKAN CINIKI

Kari akan ka’idojin Kashi na I a sama, ka’idojin da suke kasa a wannan Kashi na II suna aiki akan Abokan Ciniki mu.

Idan akwai wani tangarda tsakanin Yarjejenyar Customer da suke aiki akan ku da wannan Manufar Sirri, to ka’idojin Yarjejeniyar Customer shi zai zama a sama har iya yadda doka ta bayar kuma a lokacin da wannan Yarjejeniyar Customer ya fara aiki.

KARBA DA KUMA AMFANI DA BAYANAI

Manhajojin shiga yanar gizo na Premise domin Abokan Ciniki yana karbar bayanai da burbudin su da suka danganci shiga, tantancewa, da bayanan asusu. Sentry, Amplitude da FullStory, da wasu dillalan da Premise yake aiki dasu, zasu iya karba ko amsar bayanan ku akan abubuwan da kukeyi akan yanar gizo a lokuta da amfani da manhajojin customer na Premise. Wannan bayanan za’ayi amfani dasu ne kawai wajen inganta manhajojin Premise na Abokan Ciniki amma ba siyarwa ba ko watsawa zuwa masu amfani na waje.

Bayanan siyayya, sadarwa, da hadin gwiwa ana karbar sune a karbabbiyar hanyoyin kudi da sadarwa kamar su Salesforce, Google Workspace, da Microsoft 365, da sauran hanyoyi da aka yarda dasu da suke a sirrance da ware, wanda ma’aikatan Premise da aka yarda zasu shiga.

 

KASHI NA III – KARIN KA’IDOJI DOMIN MASU BADA GUDUNMAWA

Kari akan ka’idojin Kashi na I a sama, ka’idojin da suke a kasa sun danganci Masu Bada Gudunmawa din mu.

Manhajojin Premise na’urori ne da muke karbar bayanai akan duniyar ku. Idan kuka dauko wani daga cikin manhajojin Premise ko yin rajistar Lalitar Premise, kun yarda da karba, amfani da watsawa ko siyar da bayanan ku harda hotuna, bidiyo, rikodin, hoto da hoton allon na’ura, kamar yadda aka ayyana a wannan Manufar Sirrin kuma kun yarda cewa Premise zasu iya bayar da bayanan ku da sarrafa wannan bayanin ga abokan hulda domin amfanin su da abokan huldar su, a ciki ko waje. Za mu iya karin sanarwa akan karba da amfani dabayanan ku (harda hotuna, rikodin, hoto, hoton allon na’ura da daukar murya) acikin manhajar ko bayanan wani aiki.

KARBAR BAYANAI

Wadannan sune jerin bayanan da muke karba da dalili, kuma bisa Dokokin Sirrin Bayanai na Turai, sabida sarrafa bayanai. Za muyi Karin bayani akan bayanan ku da muke karba a sashe na gaban wannan Manufan Sirri. Idan akwai inda aka saka a wannan teburin na kasa, ku tuntube mu idan kuna bukatar karin bayani game da dokar da kuke dogara dashi wajen sarrafa bayanai.

Abin da zamu iya karba Dalilin da yasa muke karba Tushen doka (a karkashin Dokokin Sirrin Bayanai na Turai)
Manuniya, misali, suna, adieshin imel, manuniyar yanar gizo (kamar su inkiya), manuniyar mai amfani da ake canjawa wanda yake jikin wayar salula, lambobin sirri, da sa hannun na’ura Domin gane ka, domin bin Ayyukan da kuka kammala, domin magana da ku dangane da asusun ku, labarai akan Aiki da Ayyuka, domin lura da gudanar da Aikin mu, domin bin ayyuka da inganta ganowar ayyuka, domin tattara bayanai zuwa ga abokan hulda da masu alaqa, da kuma daukan mataki akan zamba.
  • Domin gudanarwa bisa kwantiragi da kai
  • Manufa bisa ka’ida
  • Ana bukata domin bin dokoki da aka gindaya (domin hana zamba)
Hotuna, bidiyoyi da rikodin, harda rikodi din sauti, hotuna da hotunan allo Domin gane ka, domin bi da tabbatar an kammala Ayyuka, domin bin ayyuka da inganta ganowar ayyuka, domin tattara bayanai zuwa ga abokan hulda da masu alaqa, da kuma daukan mataki akan zamba. Hakan yana nufin bayanai da hotuna, bidiyoyi, sautin murya hotuna da hotunan allo da kuka bayar abokan huldar mu zasu iya watsawa (abokan huldar mu ko nasu) akan shafukan zumunta da sauran su.
  • Manufa bisa ka’ida
  • Ana bukata domin bin dokoki da aka gindaya (domin hana zamba)
  • Yarda
Waje Domin gane masu yin Ayyuka, domin tattara bayanai zuwa ga abokan hulda da masu alaqa, da kuma daukan mataki akan zamba ta hanyar tantance wajen da mutum yake.
  • Manufa bisa ka’ida
  • Ana bukata domin bin dokoki da aka gindaya (domin hana zamba)
  • Yarda
ID din na’ura mai amfani da adireshin IP, kamar su operating system, saitin masu amfani, amfanin aiki da kukeyi Domin saitawa da inganta Ayyuka, harda bayar da ko shawarar abubuwa na musamman akan mai amfani a yanki.
  • Manufa bisa ka’ida
  • Yarda
Bayanin na’ura Domin fahimtar abubuwan da mai amfani ke bukata da kyau domin inganta manhaja da rahoton matsala, domin tattara bayanai ga abokan hulda da masu alaqa, da kuma tattara bayanai da za’ayi amfani dasu wajen warware tangarda lokacin da ake kammala Ayyuka.
  • Domin gudanarwa bisa kwantiragi da kai
  • Manufa bisa ka’ida
Harshe Domin ba mai amfani rubutu acikin yaren da ya fahimta ta cikin manhaja.
  • Domin gudanarwa bisa kwantiragi da kai
  • Manufa bisa ka’ida
Ma’aunin aikin APIs Domin tabbatar da ganin cewa duka APIs din da manhajar ke amfani dasu da kyau domin ba mai amfani yanayi mai kyau na amfani dashi
  • Domin gudanarwa bisa kwantiragi da kai
  • Manufa bisa ka’ida
Jerin sunayen manhajoji

 

Domin rage hatsarin yin zamba ta tabbatar da cewa mai amfani baya amfani da wani manhaja da yake canja bayanai da suke da muhimmanci wajen gudanar da aikin manhaja, misali.: bayanin waje, agogo, da sauran su., da kuma tattara bayanai daidai sabida abokan hulda da masu alaqa
  • Manufa bisa ka’ida
  • Ana bukata domin bin dokoki da aka gindaya (domin hana zamba)
Yanayin batiri Domin fahimtar tasirin na’urar mu a kan batirin mai amfani ko bibya da kuma gano masu zamba.
  • Manufa bisa ka’ida
  • Ana bukata domin bin dokoki da aka gindaya (domin hana zamba)
Data da WiFi Domin fahimtar ingancin netwok akan na’urar mai amfani da taimaka wa abokan huldan mu inganta karfin netwok, tare da yinkurin ba masu amfani aiki mai inganci bisa ingancin netwok.
  • Manufa bisa ka’ida
Idan kukayi rajistar Lalitar Crypto, muna karbar wadannan:

  • ID din mai amfani na Premise
  • ID din Lalitar Premise
  • ID din PrimeTrust Contact
  • Kasa da alamar yankin asusu
  • Duka sunaye
  • Watan haihuwa
  • Lambar waya
  • ID din haraji
  • Adireshi
  • Hoton shaidar ID na gwabnati
  • Hoton tabbacin adireshi
  • Hoton ku

Adireshin crypto na waje (Idan zaku ajiye ko tura kudin crypto daga waje)

Domin gane ku, domin lura, rikewa da sarrafa aikin Lalitar Premise da asusun Lalitar Premise din ku, domin rage hatsarin zamba, domin bin dokokin gwabnati, domin gamsar da bukatun “Sanin Abokin Huldar Ku”, domin fara bibiyar bayanai, domin fara biyan zuwa gare ku, domin tabbatar da ku da kuma na wani adireshin lalitar crypto na waje, domin fara cinikayya na kudin crypto.
  • Domin gudanarwa bisa kwantiragi da kai
  • Manufa bisa ka’ida
  • Ana bukata domin bin dokoki da aka gindaya (domin hana zamba)

 

Gaba daya, zamu dinga shigar da bayanan da mukayi a sama ne domin baku yanayi mai kyau da kuma hana masu zamba lalata Ayyukan mu, harda Ayyukan da muke biyan masu amfani da mu, da kuma cika ayyuka ga abokan cinikin mu da masu alaqa. Za’a tura wadannan bayanan zuwa Premise ta hanyar Amplitude, wani kamfanin sarrafa bayanai na waje. Wasud aga cikin bayanan da muka bayyana zamu iya watsa su ga abokan hulda, abokan ciniki da masu alaqa.

Idan kuna so ku samu karin fahimta akan bayanan da muke karba, ga kadan cikin karin bayanin:

Bayanan Da Kuke Bamu

Muna karbar bayanan da kuke bamu kai tsaye, tare da bayanan da kuke bayarwa ta asusun kamfanin waje. Muna karbar bayani idan kun kirkiri ko gyara asusu, kammala wani aiki, tuntubar masu bada taimako, ko wani sadarwa tare da mu. Wannan bayanin ya hada da suna, asusun shafin zumunta, adireshin imel, lambar waya, manunin biya, da wasu bayanan da kuka zaba ku bayar. Kuma muna karbar hotuna, bidiyo ko rikodin da kuka tura mana, harda hotuna, hoton allo da rikodin din sauti.

Bayanin Da Muke Karba Ta Hanyar Amfani Da Kukeyi da Aikin

Idan kunyi amfani da Aikin, harda Lalitar Premise idan kunyi rajistar sa, muna karbar bayani kame daku a wadannan matakan na kasa:

Bayanin Wajen Da Kuke: Idan kunyi amfani da Aikin wajen kammala Ayyukan Premise, muna karbar asalin bayanan wajen da kuke wanda yake bibiyar shigar ku wajen da sauran guraren. Idan kun ba Aikin izinin shiga ayyukan wajen ta cikin saitin na’urar ku (”platform”), kuma zamu iya asalin wajen da na’urar ku take idan manhajar yana aiki lokacin da kuka bude ko yana aiki a bayan fage. Zamu iya gano kwatankwacin wajen da kuke ta adireshin IP dinku.

Bayanin Lambobi: Idan kuka ba Aikin izinin shiga wajen da kuke ajiye lambobi akan na’urar ta hanyar tsarin izinin da wayar ku ke amfani da ita, zamu iya shiga mu ajiye sunaye da bayanan lambobi daga littafin adireshin ku domin tantance asusu, da kuma gayyata da ire-iren su.

Bayanin Karfin Batiri: Idan kuka ba Aikin damar shiga wajen bayanin karfin batiri din na’ura ta tsarin izinin da wayar ku ke amfani dashi, zamu iya shiga da ajiye karfin batiri da yanayin carji domin fahimtar yanayin wajen da kayan mu yake aiki.

Bayanin Cinikayya: Muna karbar bayanan cinikayya da ya danganci amfani da Aiki wanda ya hada da bayanan biyan kudi, kamfanin biyan kudi da kuke amfani dashi, kwanar wata da lokacin da aka gama Aiki, turawa, dubawa da biya, lokacin da ake fitar da kudi, yawan kudin da aka samu, da wasu bayanan da suka danganci cinikayya. Bayanin Na’ura: Zamu iya karbar bayani game da wayar ku, harda, misali, kalar inji, operating system da version, software da sunan fayel da version, yaren da akafi so, manuniya na daban, manuniyan talle, lambar kamfani, bayanin motsin na’ura, da bayanin netwok din waya.

Bayanin Log: Idan kukayi mu’amala da Aikin, muna karbar logs din server, wanda zasu iya hadawa da bayani kamar adireshin IP na na’ura, shiga kwanan wata da lokaci, siffofin manhaja ko shafuka da aka gani, rushewar manhaja da wasu ayyukan tsari, nau’in manhajar yanar gizo, da kuma shafi na waje ko aiki da kuke gudanarwa kafin mu’amala da wannan Aikin. Kuma zamu iya karbar aikin da kukayi a yanar gizo ko wasu ayyukan, harda bayanin manhajar shiga yanar gizo da tarihi, bayanan kaskon cookie (danganta da zabukan cookie, idan akwai), da lokutan yi.

Bayanai da Muke Karba Daga Wasu Kafafe

Idan kuka bamu bayanan asusun ku na waje ko kuma shiga cikin Aikin ta hanyar shafin waje ko aiki, ku fahimce cewa wasu abubuwan da/ko bayanan cikin wadannan asusun (“Bayanin Asusun Waje”) za’a iya watsawa cikin Asusun Premise idan kuka bada izinin wannan watsawan, da shi wannan Bayanan Asusun Waje da aka watsa zuwa Aikin ya kunshi wannan Manufa. Zamu iya hada bayanai daga wannan manhajar ko shafi da bayanan da muka karba daga wajen ku a matsayin ku na masu amfani da wannan Aikin.

Google, Branch, Leanplum, Amplitude da FullStory, da wasu dillalai da Premise yake aiki dasu, zasu iya karbar ko amsar bayani mai bayyana abubuwan da kukeyi a lokuta da duka shafuka daga Aikin da wasu manhajojin, da amfani da wannan bayanin domin tantance ayyuka da tambayoyi, gano zamba, da bayar ma’aunin ayyuka da tallece-tallece.

Premise yana daukan kariya daga zamba da bin dokoki da muhimmanci sosai. A matsayin ka’ida na cancantar jin rajista da kammala Ayyuka da Manhaja, Premise zai iya yin bibiya da binciken tsaro, domin shine daidai.

Bayani Mai Muhimmanci Akan Izinin Na’urori

Na’urorin waya sun ayyana wasu nau’o’in bayanin na’ura da manhajoji ba zasu iya shiga batare da izinin ku ba. Wadannan na’urori suna da tsarin izini daban-daban na neman izini, Na’urorin Android zasu sanar da izinin da manhajar Premise yak enema kafin fara amfani da manhajar na farko, kuma amfani da manhajar ya tabbatar da yardar ku.

AMFANI DA BAYANI

Zamu iya amfani da bayanin da muka karba awajen wadanda suka hada da hotuna, bidiyo, hoto, hoton allon na’ura domin:

    • Bayar, rikewa, da inganta Aiki, harda Lalitar Premise idan kunyi rajistar sa, harda, misali, domin yin biyan kudi, bayar da kaya da ayyuka da kuka nema (da tura bayani mai kama), gina sabon siffofi, bayar da taimako ga masu amfani, tantance masu amfani, da tura labarai na kaya da sakonnin kamfani;
    • Gudanar da ayyukan ciki, harda misali, kariya daga zamba da lalacewar Aiki, harda Lalitar Premise idan kunyi rajistar sa; domin gyaran matsalolin gudanarwa; domin sarrafa bayanai, gwaji, da bincke: da kuma lura da sarrafa amfani da abubuwan yayi.
    • Gudanar da sarrafa bayanai ga abokan huldar mu da abokan aikin su, wanda ya hada da sarrafawa kai tsaye da na’ura mai fasahar kanta takeyi;
    • Tura ko fara sadarwa tsakanin kai da tsarin taimakon mu, kamar tunatarwa mai muhimmanci da ya danganci masu amfani da manhaja;
    • Tura muku sako da muke tunanin zai baku sha’awa, harda bayani akan kayayyaki, ayyuka, talla, labarai, da taruka a Premise da wasu kamfanoni, inda an yarda kuma bisa dokokin yankin; da sarrafa Takara, sweepstake, da wasu abubuwan talla da ayyukan da ake bada lada; da
    • Saitawa da inganta Aikin, harda Lalitar Premise idan kunyi rajistar sa, harda bayarwa ko shawarar siffofi, abubuwa, gayyata, da tallece-tallece.

Doka a wajen mu na amfani da bayanan ku domin dalilan kwangila ko shari’a inda muke bukata wajen bayar da Aiki, harda Lalitar Premise idan kunyi rajistar sa, ko sarrafa shafin yanar gizo ko sabida sha’awar mu bisa ka’ida, harda duka kasuwanci da ayyukan tallece-tallece, domin dalilan bincike ko rigingimu da dalilan tallece-tallece. Inda muka dogara da dalilai wajen sarrafa bayanan ku, a karkashin dokokin kuna da damar kin yarda da wannan sarrafawa.

WATSA BAYANI

Zamu iya watsawa ko siyar da bayanan da muka karba game daku kamar yadda aka kwatanta a wannan Manufar Sirri (harda Lalitar Premise idan kunyi rajistar sa), bayanai da aka samu daga sarrafawa (harda bayanai daga na’ura mai sarrafa kansa) ko kamar yadda aka kwatanta a lokacin karba ko watsawa, harda wadannan:

    • Tare da abokan hulda da masu alaqa na Premise da suke bada ayyuka ko gudanar da karbar da/ko sarrafa bayanai a madadin mu, ko sabida tattara bayanai waje daya da / ko dalilan jigila;
    • Tare da abokan hulda da suke saka Premise tattara bayanai, hotuna, rikodin, da bidiyoyi, harda hotuna, hotunan allo, da rikodin din sauti, a yankin ku da fadin duniya;
    • Tare da dillalai, masu bada shawara, masu bada shawara fannin kasuwanci, abokan hulda masu talla, masu tantancewa, kwararrun masu bada shawara irin su kudi ko mashawarci fannin shari’a da sauran masu bada aiki da suke bukatar wadannan bayanai domin gudanar da da aiki a madadin mu ko bada shawara ko bamu aiki;
    • Martani akan neman bayani da hukuman da ya kamata idan muka yarda bayyanawar yayi daidai da, ko kuma ana bukata, da duk wani doka, tsari, ko hanyar shari’a, harda martani ga subpoenas, shedar bincike da umarnin kotu;
    • Domin kafa ko yin hakkokin doka na, ko kariya daga kaiwa kotu;
    • Domin bincike, kariya, ko daukan mataki game da zargi ko yin abubuwa marasa kyau, bijirewa Ka’idojin Amfani, ko wanda doka bai bada dam aba;
    • Domin bin dokokin da suke aiki, harda dokokin da suka shafi haraji;
    • Domin saka cigaba ko tambayoyi;
    • Tare da ma’aikatan tilasta doka, jami’an gwabnati, ko wasu na waje idan mukayi imanin ayyukan ku basuyi daidai da Ka’idojin Amfani ko wasu manufofi masu kama da haka, ko domin kariyar hakkoki, kaya, ko tsaron Premise ko wasu;
    • A hadaka da, ko lokacin cinikayyan, wani haduwa, sayar da kadarorin kamfani, karfafawa ko sake tsari, biyan kudi, ko siyan duka ko wani bangaren kasuwancin mu ga ko cikin wani kamfani’
    • Idan muka tunatar daku da, inda ake bukata, kun yarda da watsawa; da
    • Acikin halin tattara da/ko yanayin sirri wanda baza’a iya amfani dashi wajen gano ku ba.

Ayyukan Sarrafa Bayanai da Tallece-Tallece da Wasu Suke Bayarwa

Zamu iya barin wasu su bayar da aikin aunawa da sarrafa bayanai gare mu, domin yin tallece-tallece a madadin mu akan yanar gizo, da kuma bibiya da rahoto akan kokarin da tallen ke yi. Wadannan ayyukan zasu iya amfani da kaskon cookies, beacons din yanar gizo, SDKs, da wasu fasahar domin gane na’urar ku idan kuna amfani da Aikin, da kuma idan kun ziyarci wasu shafukan yanar gizo da ayyukan.

ZABUKAN KU

Bayanin Asusu

Zaku iya gyara ko goge bayanan asusun ku duk lokacin da kuka shiga asusun cikin manhaja. Idan kunaso ku kulle asusun ku, kuyi mana sakon imel akan [email protected].  Ku sani cewa a wasu halayen zamu iya ajiye wasu bayanai game da ku kamar yadda doka ta bayar, ko domin dalilan kasuwanci halattacce har yadda doka ya bayar. Misali, idan kunyi aron kudi ko bashi a asusun ku, ko idan munyi imanin kunyi zamba ko keta Ka’idojin Amfani da mu, zamu iya tsayawa mu warware matsalar kafin kulle asusun naku.

Hakkokin Shiga

Premise zai bi neman da mutum zaiyi game da shiga, gyara, da/ko goge asusun mai amfani ko wasu bayanai game da shi bisa dokokin da suke aiki.

Bayanin Wajen da Kuke

Wannan Aikin, harda Lalitar Premise idan kunyi rajistar sa, yana neman izinin karbar asalin waje daga na’urar ku daga izinin da tsarin wayar da kuke amfani dashi. Idan kun kashe karbar wannan bayanin zai rage damar shiga wannan Aikin. Amma kuma, kashe karbar asalin waje na Aikin daga na’urar ku bazai rage damar mu na karbar bayanan wajen da kuke ta adireshin IP.

 

KASHI NA IV – MAZAUNAN CALIFORNIA DA SAURAN JAHOHIN DA YA SHAFA

Wadannan jerin dokokin suna aiki akan Masu Bada Gudunmawa da Baki wadanda mazauna California da, bayan 1 ga Junairu, 2023, zuwa Abokan Ciniki mazauna California.

Hakkin Sani. Zaku iya neman da mu baku jerin nau’o’in bayanai game da ku da muka karba a lokacin da kuka bayyana (bisa doka), nau’o’in hanyoyin da aka karba, dalilan sayarwa ko kasuwanci na karba ko siyar da bayanan, da kuma nau’o’in kamfanin waje da muka ba ko siyar da bayanin. Kuma zaku iya neman da mu baku kwafi din bayanan ku da kuke bukata da muka karba na lokacin da kuke bukata (bisa doka). Mazauna California zasu iya neman sani har sau biyu acikin watanni 12, bisa iyakoki da akayi kwatance a dokoki. Domin jerin duka nau’o’in bayanai da muka karba da watsawa a watanni 12 da suka wuce, ku duba Manufar Sirri a sama.

Hakkin Gyara: Zaku iya neman a gyara kuskure a bayanan ku da muka karba.

Hakkin Gogewa. Zaku iya neman mu goge duk wani bayanan ku da muka karba daga wajen ku, banda bayanan da doka ya bamu damar ajiyewa. Idan mukayi muku martani neman gogewa da kukayi, zamu yi muku bayanin wane (idan akwai) bayanin da zamu ajiye da kuma dalili. Wannan baya aiki akan bayanan ku da babu su bisa doka.

Yadda Zaku Nemi Sani ko Gogewa. Zaku iya neman sani ko gogewa da hanyar tura sakon imel zuwa [email protected] . Idan kunyi wannan neman, zamu dauki matakai domin tabbatar da ku kafin yi. Anyi hakan domin kare bayanin ku. Zamu sa ku bamu adireshin imel dinku. Idan kuna da asusu da mu, dole yayi daidai adireshin jikin asusun ku da mu. 

Wakili Mai Izini. Zaku iya saka wakila da izinin ku ya nema a madadin ku. Zamu nemi tantancewar cewa ku, kuka ba wakilin dama. Saidai idan doka yace ba haka ba, dole wakilin ya bayar da bayanan tuntubar ku. Zamu tuntube ku domin tabbatar ku ba wakilin izini. Da zaran mun tabbatar, zamu yi abin da kuke nema da wuri.

Babu Siyar da Bayanai ba Tareda Izini ba. Bama siyar da bayanan Baki ko Abokan Ciniki. Zamu iya siyar da bayanan Masu Bada Gudunmawa ga kamfanin waje tare da yardarm ku kuma kamar yadda aka kwatanta a wannan Manufar Sirri kadai.

Babu Nuna Banbanci: Kuna da damar kin yarda da nuna banbanci wajen damar da kuke dashi.

Hakkin Mazauna California Neman Bayani Dangane da Bayarwa Zuwa Kamfanonin Waje Sabida Dalilan Tallace-Tallace. Zaku iya neman bayani akan bayarda bayanan ku zuwa kamfanonin waje ko kamfanoni masu alaqa damu domin dalilan tallace-tallace. Domin yin wannan neman, kuyi mana sakon imel ta [email protected] . Kuyi hakuri ku jira har tsawon kwanaki 30 domin sarrafa neman naku. Zaku iya irin wannan neman sau daya a shekara.